MAGUNGUNAN DA ZOGALE KEYI



HAKIKA ZOGALE WANI NAU'IN

ICCENE DA ALLAH MADAUKAKIN

SARKI YA TSIRAR DASHI ADORON

KASA,DOMIN MUTANE DA ALJANNU

DAKUMA DABBOBI SU AMFANA

DASHI,KAI HATTA ITA KANTA KASA

TANA AMFANA DA ICCEN ZOGALE

WANDA YAFITO DAGA

CIKINTA,WANI ABIN BAM MAMAKI

SHINE IRIN YADDA

HALITTUNRUWA

SUKE AMFANA DA SAIWAR ZOGALE

DA TAKE AKUSA DA WANI GULBI

KO

KORAMA.........

YANA DAGA CIKIN CUTUTTUKANDA

ZOGALE YAKE WARKARWA KAMAR

HAKA::-----

1. Ana dafa ganyen zogale da

zuma asha kamar shayi,domin

maganin Olsa(ulcer).

2. Ana shafa danyen ganyen

zogale akan goshi,domin

maganin ciwon kai.

3. Ga wanda ya yanke ko ya sare

kowani karfe yaji masa ciwo,zai

shafa danyen ganyen zogale

Insha Allah jinin zai tsaya.

4. Ga maifama da kuraje ajiki,ya

hada garin zogale da man zaitun

ya shafa.

5. Anasa garin zogale akan wani

rauni ko gembo,domin saurin

warkarwa.

6. Sanya garin zogale aciki acikin

abinci yana maganin Hawan jini

dakuma karama mutum kuzari.

7. Ana dafa ganyen zogale tareda

sa kanwa yar kadan,domin

maganin ciwon shawara.

8. Ga mai fama da ciwon ido zai

digaruwan danyen

zogale,hakama mai fama da

ciwon kunne.

9. Macenda ke shayarwa ta dafa

furen zogale da zuma,don karin

nono.

10. Wanda ke fama da yawan

fitsari wato cutar Diyabetis ya

rinka shan furen zogale da citta

kamar shayi.

11. Idan aka tafasa furen zogale

da Albasa akasha kamar shayi

yana maganin sanyi.

12. Hakama cin danyen zogale

yana maganin tsutsan ciki ga

yara.

13. Ana daka ganyen zogale da

'ya'yan 'baure asha da nono ko

kunumaganin ciwon hanta ko

koda.

14. Ga mai fama da sanyin kashi

ko wani kumburi zai soya 'ya'yan

zogale adakasu sannan ahada da

man kwakwa,sai ashafa.

15. Adaka zangarniyar zogale da

'ya'yan dake ciki tareda

kananfari,citta ,masoro da

kimba,domin karin karfin da

namiji dasa masa kuzari

hakakuma yana karawa mata

Nishadi.

16. Adaka saiwar zogale da

'ya'yan kankana asha da nono

maganin tsakuwar ciki(wato

Apendis).

17. Haka kuma idan Aljani

yabugar da mutum ya zube to

ana shaka masa ganyen zogale

ahanci,za'aga yayi saurin rabuwa

da mutum kokuma aga yayi

magana shi Aljanin.

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/HYg2KvNxf2kI2IuVfqh5RH


SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 
https://www.facebook.com/netage001/

Telegram channel

0/Post a Comment/Comments

Previous Post Next Post

header

Sponsor