Amfanin Lemon Tsami A Jikin Dan’adam


Amfanin Lemon Tsami A Jikin Dan’adam:

Lemun tsami yana da mutukar amfani ga lafiyar dan’adam. Ga wasu daga cikin amfanin lemun tsami da kuma yadda ake amfani da shi.


Gyara Fuska: Ana amfani da Lemun tsami wajan kauda kurajen fuska, fimfus da kyasfi, yana saka fuska ta kara kyau. Yadda ake amfani da shi, araba 1-2, rabin za a goge fuska da shi, za a yi haka na wasu lokuta, amma a kiyaye idanu, kuma kar a shafa a shiga rana sai an wanke tukunna.

KARANTA:


Dattin Hakori Da Warin Baki: A yi amfini da burushin wanke baki da ruwan lemun tsami a wanke hakora zu su fita kar, baki zai bar wari, amma kar a rika wankewa akai-kai sai lokaci saboda zai iya raunana karfin hakori.


Warin Kashi (Hammata): Idan ana fama da ciwon warin kashi, ko rashin tsaftace hammata yadda ya kamata, idan an shafa lemun tsami a hammata zai kauda wannan warin.


Rage Kiba Da Timbi (Teba): Wanda ke bukatar hakan, ya samu lemun tsami daya a ruwan sha da bai wuce kofi daya ba, lokaci-lokaci, kiba da taiba za su tafi.


Rauni (Ciwo): Sabon raunin da bai wuce hankali ba, da zarar an matsa mai lemun tsami zai kame ya warke.


Rage Sha’awa: Ana shan lemun tsami da lipton dan rage sha’awa.


Makyankyaro: Idan goge makyankyaro da lemun tsami akai-akai zai mutu.


AMOSANI: Ana goga lemun tsami a kai bayan an aske gashin kai.

Karni: Ana amfani da lemun tsami wajan kawar da karnin kifi. Amma a kula, idan mace ta yawaita amfani da lemun tsami to zai rage mata sha’awa. Haka mata masu ciki ka da su yawaita amfani da lemun tsami.

Masu genbon ciki wato olsa, suma su kula wajan shan lemun tsami. Amma dukkan wadannan zai musu illa ne idan sun sha a ciki ba wai shafawa ba.

Yadda Ake Amfani Da Lemun Tsami Wajan Gyaran Fata Lemun tsami da zuma; a debi rabin cokalin ruwan lemun tsami da kuma rabin cokalin zuma sai a kwaba su, daga nan a shafa a fuska na tsawon minti 15, sannan a wanke da ruwan sanyi. Idan ana da fata mai gautsi to za a iya hadawa da man zaitun.

Lemun tsami da nono; za a hada rabin cokalin ruwan lemun tsami da rabin nono (amma an fi son kindirmo) sai a kwaba sosai. Bayan haka, sai a shafa a fuska.

Man Lemun Tsami Man lemon tsami yana da mahimmanci sosai musamman ma a fata.

Domin yana dauke da sinadarin bitamin C. Wannan sinadarin kuma yana kara lafiya ne a jiki da fata. Man yana warkar da kurajen fuska da kwarkwata. Yana taimakawa wajen kara wa fatar fuska haske ba tare da yin bilicin ba. Uwa uba kuma yana taimakawa wajen magance mura. Ana amfani da man ‘sunscreen’ idan za a shiga rana. Ka da a shiga rana da man lemon tsami a fuska domin zai iya illata fatar. Don haka an fi son a shafa shi da safe ko da yamma domin samun sakamako mafi inganci.


Yadda Za A Hada Man Lemon Tsami A samu lemon tsami sai a bare fatar ka da a yi amfani da ruwan lemon tsami wajen hada man lemon tsami. Sannan sai a samu man kwa-kwa, bayan an bare bawon, sai a shanya a karkashin fanka kamar tsawon awa daya. Bayan ya dan bushe, sai a saka a gora sannan a zuba man kwa-kwa a gauraya bawan da man a gorar sannan a rufe.

Sai a samu gurin da babu rana ko daki ko kicin a ajiye kamar tsawon sati biyu. Amma a kullum a rika zuwa ana girgizawa. Shi ke nan! Man lemon tsami ya samu.


Za a iya amfani da man zaitun ma idan babu man kwa-kwa.


Idan ba za a iya bin wannan hanyar ba akwai wata hanya da za a bi don hada man lemon tsami.



A sa bawon a tukunya sannan sai a zuba man kwa-kwa a dora a wuta amma ka da wuta ta yi yawa.

A rika gaurayawa tsawon minti biyar. Bayan haka, sai a sauke ya huce sannan sai a zuba a kwalba.

0/Post a Comment/Comments

Previous Post Next Post

header

Sponsor