YADDA AKE GYARAN JIKIN AMARYA




KAYAN HADIN GYARA JIKIN AMARE

( fatan ta yi laushi da sheki)

man zaitun

lalle

kur-kur

madara peak




Zaki hade wadannan kayan hadin guri daya, sai ki kwaba su ki shafe jikinki da fuskarki, zakiyi wannan hadin kafin ki shiga wanka. Idan ya bushe a jikinki sai ki murje sannan sai ki shiga wanka jiki yana yin kyau yayi sheki




GYARA JIKI 2:




Wannan hadin shi akecewa kafi TURAWA


kur-kur

dulka

zuma

kwai

lemun tsami

Karanta:

Ki hade su guri daya ki samu ki kwaba kamar yadda ake kwaba lalle, amma yafi kwabin lalle ruwa, sai ki shafe fuskarki Idan kuma har dajiki kikeso, sai ki shafa harda jiki

Bayan (1hr) sai ki shiga wanka zaki ga yadda jikinki zai goge




GYARA JIKI 3

( fata ta yi laushi da sheki)




lalle

kwaiduwar kwai guda 3 ( yellow )

manja cokali 3

kur-kur

Sai ki kwaba su guri daya ki shafe jikinki zuwa (1hr) daya, sai ki yi wanka da ruwan zalla da ruwan dumi ki shafe jikinki da ita sai ki kuma yin wanka



KYAN FUSKA:


Sai ki hade su guri daya ki kirba su cikin turmi, ki mulmula ki rinka wanke fuska zaki ga yadda fuskar ki zatayi

dettol

sabulun Ghana

garin zogale

farar albasa


KARANTA:

GYARA FUSKA;


Wanna hadin wanda ya kesa fuska tayi haske da annuri takun Kore kurajen fuska.

bawon kankana

A samu bawon kankana sai a rinka goge fuska da shi yana gyara fuska tayi sumul



GYARA FATA

Lemun tsami

bawon kwai

kur-kur

Zaki hade su guri daya ki daka su sai ki rinka wanka dashi fatar mace zata goge tayi kyawun gaske




GYARA FATA:

ganye magarya

sabulun salo

Zaki daka ganyan magarya sai ki zuba a cikin sabulun salo ki rinka wanka yana gyara jiki




GYARA FATA

• ganyan magarya

• man zaitun

• man habbatussauda

Ana daka ganyan magarya a zuba cikin man zaitun da man habbatussauda shi ma yana gyaran




GYARA FATA


lalle

garin ridi

Ana amfani da lalle kafin ki shiga wanka sai ki kwaba ki zuba garin ridi ki shafe jikinki zuwa (1) hr sai kiyi wanka




GYARA GASHI


Man zogale

Man kwakwa

Man zaitun

Zaki hade su guri daya ki rinka shafawa a kanki




GYARA GASHI

Man zogale

Ganyan magarya

Kanunfari kadan


Sai ki hade su guri daya ki rinka shafawa a kanki yana sanya tsayin gashi ya kuma yi laushi



GYARA KAFA:

Baki ba zuwa wajen wanke kafa madarar kinyi amfani da wannan hadin

man shanu

man kwakwa

man ridi

man alayyadi

Idan kafa tana tsagewa ko tana kaushi da daddare zaki hada wadannan mayamayen guri daya ki shafa a kafa in zaki kwanta bacci daddare sai ki daure da Leda da safe ki wanke da ruwan dumi ki shafa man zaitun da man ridi


MAGANI CIWON SANYI


Duk macen data ke son ni'ima ta tabbatar mata, koda yaushe ta kasance cikin ni'ima to lallai ya zama dole ta magance matsala ciwo sanyi


TOILET INFECTION

Domin magance wannan matsala ta samu wadannan kayan


hulba

bagaruwa

habbatussauda.


Ki hada hulba da bagaruwa guri daya, ki dafa idan ruwan ya sha iska sai ki zauna a ciki, kuma ki samu man habbatussauda kiyi matsi dashi.

Kiyi sharing da kawayenki don su amfana

0/Post a Comment/Comments

Previous Post Next Post

header

Sponsor