YADDA AKE DADEWA A KWANCIYAR AURE



yadda ake dadewa a kwanciyar aure:




MA'AURATA ONLY:




Hanya ta daya: a shiryawa saduwar:




Hanya ta biyu: ka kwantar da hankalinka ko ka rage sauri:




Hanya ta uku: samun kwarin gwiwa.




Kussan duk mutum daya a cikin uku suna fama da saurin yin inzali ko kuma saurin gama saduwa ba’a lokacin da matar ko mijin yake so ba. Duk da cewa akwai magunguna da za’a iya amfani dasu wajen magance wannan matsalar, amma akwai hanyoyi da idan mutum yabi zai sami sakamako mai kyau.




A takaice

Zamu tattauna akan wadannan abubuwan:

- Ka gano tsakar PC.

- Ka tsaya daga saduwa.

- Kuyi wasa kafin saduwa.

- Chanza yanayi.

- Kayi a hankali.

- Ka gwada hanyar 7 da 9.

- ka gwada hanyar jinkirtawa da kuma matsawa.

- Karfafawa kanka gwiwa.

- Ku tattauna da matarka.

- Ka nemi shwarar likita.




Hanya ta daya: a shiryawa saduwar




1. Ka gano tsakar PC. Akwai wata tsoka dake tsakanin mafitsararka da kuma duburarka. Idan kana san nemo wannan tsokar ta PC, zaka shiga bandaki ne domin yin fitsari, kana cikin yin fitsarin sai kayi kokarin tsayar dashi, wannan tsokar da kayi amfani da ita wajen tsayar da fisarin, itace tsokar PC da ake magana.




Ka bawa kanka lokacin domin da dame wannan tsokar ta hanyar mosta ta ta hanyar d’ame ta. A kalla yana da kyau ka mosta ta sau 15 a rana domin ya taimaka maka da dare. Hakan zai taimaka maka wajen kiyaye lokacin da kake son yin inzali.




2. Ka tsaya daga saduwa. Akwai mutanen da suke bukatar su dan daina saduwa na wani lokaci. Kuyi magana da matarka sannan kuma ku tattauna da likitanka akan matsalar ka. Amma bana nufin ka daina kula matarka ba, zaku dinga wasa na soyayya amma kuma banda saduwa. Hakan zain koya maka yadda zaku zauna cikin farin ciki ta hanyar dauke maka cewa dole sai kun sadu.




Hanya ta biyu: ka kwantar da hankalinka ko ka rage sauri:




3. Kuyi wasa kafin saduwa. Saduwar aure wani irin abune mai ban mamaki. Kowa ya sani cewa namiji yana yin duk wani abu domin kar yayi inzali da wuri, ita kuma macen tana yi duk wani abu domin tayi inzali da wuri.




Saboda haka, ku dinga wasanni kafin saduwa kamar sumbata, amfani da baki, da sauran abubuwan da baza’a rasa ba. Hakan zai taimaka wajen bawa matar gamsuwa.




4. Chanza yanayi. Yana da kyau ku dinga chanza yanayin kwanciya lokaci bayan lokaci domin hakan zai nuna maka wasu abubuwa da baka sani ba a baya na jin dadi.




Wata hanyar chnaza yanayin kwanciya shine idan kuna tsakiyar saduwa. Da zarar kaji zakayi inzali, kayi sauri wejen chanza yanayin kwanciyar.




Daya daga cikin yanayin da zai taimaka anan shine idan macen tana samanka.




5. Kayi a hankali. Ka dinga bawa kanka lokaci tsakanin shiga da fita da kake yi misali kamar sakanni uku tsakani. Kar ka dinga sauri ko gudu domin hakan zai sa kayi inzali da wuri.

- Duk lokacin da kaji zakayi inzali, sai ka rike a ciki har ka samu nutsuwa sannan ka ci gaba.

- Wata hanyar daina sauri itace ka dinga amfani da sauran bangarorin jiki ta hanyar tabawa ko sumbata.




4. Ka gwada hanyar 7 da 9. Akwai abinda masana suke kira da 7 da 9, yadda akeyi shine ka shiga ka fito da sauri sau 7 sannan kuma ka shiga ka fito a hanka sau 9. ka ci gaba da yin hakan har ku gama a ranar.




5. ka gwada hanyar jinkirtawa da kuma matsawa. Wannan hanyar tana bukatar matarka ta taimaka maka wajen matsa gaban naka a lokacin da kaji alamar zaka yi inzali musamman kusa ka kan. A rike shi a wasu ‘yan sakanni har sai kaji ka daina jin cewa zakayi inzalin, sai ka jira sakanni kamar talatin sannan a koma yin wasan soyayya kuma.




Hanya ta uku: samun kwarin gwiwa.




6. Karfafawa kanka gwiwa. Zaka iya bawa kanka kwarin gwiwar cewa zaka iya yin abinda kake so. Da zarar ka fara jin cewa ka karaya, sai ka daina tinanin karayar ka koma tinanin jin dadin da kakeyi da kuma cewa tabbas zaka iya dadewar da kake so.


KARANTA:

7. Ku tattauna da matarka. Yana da kyau ku zauna kai da matarka domin kuwa tana da hakki na ka dinga gamsar da ita wajen saduwa. Idan da baka saurin inzali sai yanzu ka fara, zata iya yiwuwa matsalolin da suke faruwa ne a tsakaninku wanda zaku tattuna domin magance ta.




- tattaunawa tare da ita zai sa ta baka shawarwari da take tinanin zasu taimak muku wajen dadewa. Misali, chanza yanayin kwanciya, chanza yadda kuke wasannin soyayya da sauransu.




8. Ka nemi shwarar likita. Zata iya yiwuwa kana da wata cuta ne a jikinka wanda take sawa kake saurin yin inzali. Saboda haka, likita zai duba ka sannan ya fada maka abubuwan da ya gano a kanka.








0/Post a Comment/Comments

Previous Post Next Post

header

Sponsor