YADDA AKE KULA DA LAFIYAR JARIRI





YADDA AKE KULA DA LAFIYAR JARIRI:

Anan idan nace jariri ina nufin yaro karami daga haihuwa zuwa lokocin da za'a yaye shi...

Da zaran an haifi yaro me yakamata ayi masa ?

Zan kawo wannan bayani ne sabida wassu matan zun zabi su haihu a gidajen su fiye da zuwa asibity duk da hatsarin dake cikin haihuwa a gida.




1- Da zaran an haifi yaro abu nafarko da yakamata a duba shine:

-A duba aga ko yaro yana numfashi daidai 

Yin hakan gaskiya zai taaimaka wajen ceton rayuwar jarirai.

Mafi yawa jarirai suna samun matsalar numfashi lokocin da aka haifesu, rashin duba lafiyar numfashi a wannan lokocin yana aika jarirai zuwa Lahira...

Zai dai kiji ance ta haifi yaron da rai daga baya ya koma ga ALLAH...

Abin tambaya idan jariri baya numfashi mekyeu ko baiyi kuka ba me yakamata ayi ?

A daidai wannan lokocin diyawa daga cikin ungozoma da ma'aikatan lafiya zai kiga suyi ta dukan bayan jariri, wanda hakan ba daidai bane, masana kiwon lafiya sun hana...

Maimaikon a daki jariri to ayi haka:

- A share majinar dake bakin jariri, a bude bakin jariri as yatsa ko sirinji a share majinar dake bakin sa.

- A ringa shafa bayan jariri a hakankali, hakan zai dumama jikin jariri har yasamu yaji garau..

- a lokaci guda a rika k shafa ƙarƙashin ƙafar jariri, hakan zai taimaka wajen saka jariri yaja ƙaƙƙarfan numfashi.

Bayan anyi haka idan jariri bai kawo wuta yadda akeso ba, to dole ayi masa Busar Numfashin Ceto, wanda babu bukatar bayani domin aikin ma'aikacin lafiya ne...

Idan kuma akayi sa'a aka samu numfashin yaro kalaw yake..



2- Abu na biyu shine dole a kifa yaro a kirjin mamar sa ( skin to skin contact):

Diyawa daga cikin mutanen mu da zaran an haifi jariri abu nafarko da sukeyi shine suyiwa jariri wanka, wanda hankan shine hanyace ta zuwa lahira ga jariri..

Sabida a daidai wannan lokocin wanka zai iya sa ya kamu da matsanacin sanyi.

Jariri baya buƙatar wanka bayan haihuwa nan take, abinda yake bukata shine waje mai dumi...



3- Bayan hakan abu na uku shine.

A taimaka a saka jariri a nono da zaran angama wadannan abubuwa guda biyu domin Ya samu nonon farko mai dauke da maiko..

Sabida fa nonon farko Yana dauke da sinadaran bada kariya ga jarirai..



4- Abu na hudu shine: Allurar rigakafin BCG Da Hepatitis B Vaccine.

Da zaran sun fita a labor room ayiwa jarirai rigakafin tarin fuka TB da kuma ciwon hanta kafin suje gida.

Dalilin yin hakan idan fa suka fita daga asibity zuwa gida anan ne mutane za sufara barka kuma kowa burin sa yadauki jaririn wanda sabon mutum ne babu ishesshen garkuwar jiki a garesa, ta nan zai iya daukan wadannan cututtukan idan ba'a masa riga kafin ba.


5- Abu na biyar shine: A karbawa yaro maganin ciwon ido na tetracycline eye ointment a inda saka masa.


Dalili kuwa shine yanzu cutar sanyi irinsu gonorrhea da chlamydia sa sauran infection yayi yawa.

Wanda idan macce tana dauke da wannan matsalar zai iya shaifar idon jaririn ta, shine dalilin bada maganin.

6- Abu na shidda shine : A tsaftace jariri a goge duk wani jini dakuma kashin farko na jaririn, amma kada ayi masa wanka a ranar da aka haife shi.

Bayan an goge shi a samu kaya mai kauri a saka masa, idan babu kauri za a iya saka masa riga biyu a lokoci guda.

Sayan kwana biyu ko uku sai aringa yiwa jaririn wanka akai akai, domin gusarda nono, yawu, da kuma sauran datti.

Ina bayani ko rabi banzo ba lokocin da na daukawo kaina ya cika.

Mahaifiya da jaririn suna da bukatar kulawa ta musamman bayan haihuwa.

Yana da kyeu mahaifiya da jaririn ta sudinga xuwa *Postnatal* , ana a duba jariri da mahaifar sa :

- Kwana daya da haihuwa

- Kwanaki uku da haihuwa

- Kwanaki bakwai da haihuwa


Dalili wannan zuwa shine domin a gane da wuri idan da akoi wata matsalar kuma ayi maganin ta ( early diagnosis and treatment).

Kusan dai yawan zuwa asibiti ita ce mafi kyawun hanyar gano matsalolin lafiya kafin su zamo hatsari, Ba a tsaya ana tambaya ta Facebook ko WhatsApp...

Ga wassu daga cikin alamomin da idan aka gani kada a tsaya a gida a gaggauta zuwa asibiti domin neman shawarar likita:

KARANTA:


1- Numfashi da sauri da sauri

2- Numfashi Dakkyer

3- Zazzabi

4- Kin cin Abinci

5- Fita daga hayyaci

6- Amai da Gudawa




Wadannan su muke kira da *danger sign* ma'ana alamomi masu hatsari ga jariri, sabida yanxu zai aika jariri zuwa kabari..

Idan aka ga É—aya daga cikin waÉ—annan alamomin hakan na nufin bashi da lafiya.




Idan jaririn yana da alamomi samada alama ɗaya, to yana cikin babban hatsari kuma yana buƙatar ganin likita da gaggawa.

Mu ma'aikatan lafiya matsalar da akafi zuwa da shi wajen mu shine:




1- Yawan kuka

2- Amar da Nono

3 Rashin Bushewar Cibiya

4- Kumburin ciki




1- Yawan kuka:




Waɗansu jariran sukanyi kuka sama da wasu. Jaririn dake kuka wataƙila lafiyarsa ƙalau idan har wani alamar rashin lafiya bai bayyana a jikin sa ba.




Amma duk sanda aka ga yaro yafiye kuka kuma babu sauran alamomin rashin lafiya a duba ko yana numfashi dai dai alokacin da baya kuka.




Akoi yawan kuka da muke Kira da *Colic* amma shi mafi yawa yaro daddare yake yawan kukan, kuma yaro yana dainawa bayan watanni uku.




2- Amar da ruwan nono:




Jarirai sukan yi tunbiɗin nono. Wani lokacin dayawa har yakan fito ta baki ko hanci. Tunbiɗin nono ba matsala bace matuƙar jaririn yana yawan shan nono, kuma yana ƙara nauyi. Yi ƙoƙarin riƙe shi a tsaye bayan yasha. Wannan zai hana nonon ya fito.




Amai Wanda take bukatar zuwa asibiti sune:




- Amai ba ƙaƙƙautawa, ko kuma ya kasa riƙe komai acikinsa.

- Aman jini.

- Kuraje




3- Rashin Bushewar Cibiya:




Bayan an yanke cibiya kada a dinga rufeta.




Kada a saka kashin shanu, ko gawayi, kada rufe ta da kaya ko kunzugu. Kada a rika taba ta, kuma idan ya zama dole a taba to a wanke hannaye da sabulu da ruwa kafin a taba.




Idan cibiyar ko cikin yayi datti, ko kuma busashshen jinni ya makalkale a jiki, sai a wanke da sabulu a kuma goge da kyalle mai tsafta.




Idan mahaifiya tanaso ta rufe cibiyar to a tabbatar abin da za a rufe din mai tsafta ne, kuma a rika canjawa duk bayan lokaci-lokaci a kowacce rana.




Idan aka bi wannan tsarin to Cibiyar zata bushe ta faÉ—i a cikin sati.




Idan kewayen cibiyar yayi ja ko zafi ko yana wari ko yana fitar da ruwa, to wataƙila ta kamu da cuta ya kamata aje asibity.




4- Kumburin Ciki:




Mafiyawan matsalar kumburin ciki, ba matsala ce da take bukatar magani ba, shawarwari kawai ta wadatar.




Mafi yawa mata basa barin bakin nono ya Shiga bakin yaro sosai ba, hakan zai sa yaro ya tsotsi iska, Kuma wannan iskan yana taruwa ne a ciki har ya kumburar da cikin.




Idan aka gyera yanayin shayarwa bai daina ba aje asibity domin bincike.




5- Kuraje




Sababbin haihuwa suna yin ƙuraje, ruɗi-ruɗi dakuma banbancin launin fata wanda sau dayawa basa cutarwa kuma suna washewa da kansu.




Ƙuraje a ɗuwawun jariri yana faruwa ne saboda kasancewar su cikin danshin fitsari da kashi. A riƙa goge wurin akai-akai. A riƙa canja wando akai akai . Za a iya shafa Dustin powder zai taimakawa. Idan bai warke ba acikin 'yan kwanaki to ya kamata aje asibity.








Shayar da Jariri nonon uwa zalla






Watanni shidda na farko yana da kyeu a shayar da jariri nonon uwa zalla ba tareda an hada da, ruwa, kunu, abinci ko magani ba ( magani ni ma ana badawa ne idan yazama dole kuma saida izinin likita)




*Yaya ake shayar da jariri nonon ?*




Mai jegon (da bata taɓa haihuwa ba) zata iya buƙatar taimako wajan shayarwa. A taimake ta ta sami nutsuwa. A tallafe ta da abin shimfiɗa da filo domin ta zauna sosai cikin jin daɗi.




A faɗawa 'yan gida da sauran baƙi da su ɗan barta ita kaɗai tare da jaririn. A ƙara mata ƙwarin gwiwa. A hankali shayarwar zata yi mata sauƙi.

Tambayoyi da muke samu duk lokocin da muka gabatar da shiri akan shayar da yaro nonon uwa zalla shine:




*Ance nonon uwa zalla a watanni shidda na farko baya idan jariri* ?




Kada ki bari wani ya gaya miki ai baza ki iya samar da isashshen nono ga jaririn ki ba, musamman ma a watanni shidda na farko.




Tabbas wassu uwayen baza su yarda da wannan zancen ba dole sai sun hada da:

- Ruwa

- Abinci

- Kunu

- Madarar Gwangwani

- Ko Kuma wani nauyin Abinci.

Irin wannan nau'in na abinci bata kuÉ—i ne kawai, kuma Yana da illa sosai ga Lafiyar jariri.




Jariri mutum ne mai rauni wato ba su da garkuwar jiki mai karfi da za ta iya yakar cuttukan masu saurin dauka ta hanyar abinci.




Sabida haka wadannan abincin zai iya musu illa sosai.




Daga cikin illolinsa akoi haifar da gudawa ga jariri. Gudawa tana sa jariri ya rage nauyi ya kuma yi rauni.




Kuma amfani da irin wannan nau'in na abinci yanasa samar da nonon mahaifiyar ya ragu. Wannan zai sa ta dad tabbatar da cewa bazata iya shayar da jaririn da nono ba kaÉ—ai.

Diyawa daga cikin mata sai su kawo maka uzirin babu ishesshen ruwan nono.




To ya kamata kusan cewa iya yawan shayarwarki iya yawan ruwan nonon da zaki samar.




Kuma a rika yawan shan abu mai ruwa ruwa (kaman kunun alkama ko shinkafa) kuma ki ci abinci mai yawa.




Sai kuma yawan hutu. shi yasa dabiyar mu ta Hausawa ta burgi ne idan mace tahaihu komai yi mata ake, hakan nada kyeu yana taimaka wajen samar da ruwan nono.

Za mu kawo kadan daga cikin amfanin shayar da nonon uwa zalla zuwa watanni shidda na farko wanda hukumar lafiya ta duniya da sauran kungiyoyin lafiya suka tabbatar, Gasu kamar haka :




1- Yana Karawa jarirai basira.

2- Yana Kara musu garkuwan jiki.

3- Yana karesu daga cututtuka.

4- Yana Kara musu Ilmi.

5- Yana Hana yaro mummunar kiba da mummunar ramewa.

6- Yana Kara soyayya tsakanin uwa da da.

7- Yana dauke da dukkan nau'in abinci da jariri sabuwar haihuwa yake bukata

8- Yana kare uwa daga kamuwa da ciwon jeji dakuma raunin kashi a karshin rayuwar ta.

9- Yana taimakawa wajan tsaida jinin haihuwa.

10- Yana taimakawa wajan hana É—aukar ciki




Wadannan kadan daga ciki kenan...

Insha ALLAH zamu ci gaba zuwa wani lokoci...

Idan da mai tambaya muna sauraro...




Tambaya:

Mardiya Sani:

Dr. Dan Allah me yake sa nonon uwa daukewa lokaci zuwa lokaci se taji babu ruwan nono ko kadan da jariri ze sha ?




Amsa:




-Rashin shayar da jariri akai akai.




- Rashin Cin Abinci masu gida jiki ( ana ciyar da jariri ne ta hanyar ciyar da kan ki.)




- Rashin hutu Yana kawo wannaan matsalar.




- Wassu magunguna da muke amfani da su over the counter, mun daukesu kamar abinci ba tareda munsan illar sa ba.




-Sai kuma wassu cututtuka suna iya kawo wannan matsalar




Shawara idan anbi ka'idodin ya gagara ya kamata aje asibity shine amfanin postnal da ake zuwa.




A gaskiya idan muka duba yadda ake samun yara kanana masu fama da ciwon yunwa masu yawan gaske, akoi bukatar karantar da iyaye matakan kula da jarirai domin samar da yara masu koshin lafiya.




MATAKI NA FARKO:




- A shayar da yaro nonon uwa zalla har zuwa watanni shidda , ba tareda anhada da ruwa ba.




- Da zaran yaro ya tashi a bacci a saka yaro a nono, a wannan lokocin ba wasa yake bukata ba.




- A tabbatar lokocin lokocin da aka saka yaro a nono yazama bakin nonon ya shiga bakin yaro sosai. Idan bai shiga sosai ba, yaro bazai samu ruwan nono yadda yakamata ba. Kuma hakan yana kawo kumburin ciki, Kullewar ciki, kukan ciki da yawan tumbudi.




- Kuma idan aka saka yaro a nono kada ayi gaggawar cire shi a bari ya sha sai ya koshi ya bari da kansa. kuma kada kada ayi gaggawar canza masa nono abari yasha daya nonon sosai kafin a canza masa.




- Bayan angama ba yaro nono kada a maida nono sai ansa ruwa ko tsuma mai lemar ruwa inda hali mai dumi a goge bakin nonon. Rashin yin haka yana bada dama ga kwayoyin bacteria su samu zama a bakin nonon yakawo matsalar zawo ga yaro.




MATAKI NA BIYU:




- Duba ga al'adun kasar mu, musamman nan Arewa akai yara allurar rigakafi akan lokoci domin kula da lafiyar su musamman Wadanda ake ma yara da zarar haihuwa irin su BCG, HBV da OPV 0 domin kare su daga hatsarin ka muwa da kwayar cutar tarin TB, ciwon hanta rukunin B da kuma cutar shan inna.




- Dabi'ar mu anan arewa shine idan mace ta haihu ana samun mutane Yan barka dake tururuwar zuwa ganin jariri kuma su dauki yaro wassu har su sa yatsa a bakin yaro ba tareda sanin wacce irin cutar suke dauke da ita ba, sabida haka yin rigakafi akan lokoci na da amfani.




Rashin yin rigakafi ga yara yana maida koshin lafiyar jariri baya fiye da kashi 70.




A takaice dai ga na'ukan rigafin da akeyi ga yara anan kasar mu Najeriya kyeuta:




- Tarin TB

- Cutar hanta

- Shan inna

- Tarin kototo

- Tsarka hakora

- Tarin nimoniya

- Tarin influenza

- kyenda

- shawara

- cholera .




Idan yaro ya shiga watanni shida ana bada Vitamin A domin Karin lafiya ga ganin ido, da kuma kariya.




Haka lokocin da yaro ya shiga watanni 12 ana bashi Albendazole domin kariya da kuma magance tsotsan ciki.




MATAKI NA UKU:




- Da zaran yaro ya cika watanni shidda nonon uwa zalla bazai ishe shi ba dole sai anhada da abinci da ruwa.




- Lokocin da yaro ya cika watanni shidda a tabbata abincin da za abashi mai ruwa ruwa ne kuma yana dauke da sinadaran Nutrient)




- Maganar Idan ana bawa yaro Kwai idan ya girma zaiyi dauke dauke karya ne, yaro yana bukatar kwai, kifi, nama, kayan itatuwa da sauran su.




- Mafi yawa garin kunun da ake hadawa yaro ba nutrient bane, Yana dauke da sinadaran Carbohydrate ne kawai.




Ka hanyoyin da za kubi ku hada garin kunu mai dauke da sinadaran Nutrient a sauwake:




1- A samu Gyero ko masara ko shinkafa ko alkama ko dawa alal misali Kopi shidda (6). an samu sinadaran carbohydrate .




2- A samu Wake , ko waken suya Kopi uku (3) ansamu sinadaran protein.




3- Asamu Gyeda Kopi 1 ko 1.5 (Kopi daya ko daya da rabi ) ansamu protein, fat & oil.




A gyera su gabaki daya sannan adan soya shi sama sama sai a nika yazama garin kunun yaro.




MATAKI NA HUDU:




Diyawa idan aka yaye yaro yana komawa baya, yana rashin lafiya sosai.




Gaskiya yaye yaro lokoci guda kuskure ne babba, akoi hikimomi da ya kamata ayi amfani wajen yaye yaro.




Hikimar itace:




Idan ana bawa yaro nono so biyar a rana sai mayar so 4 a rana yauda gobe za amayar so uku , haka yauda gobe sai amayar so 2, za a ga kafin a maida so daya baima damu da nonon ba, zai yaye kansa da kansa tun kafin a yaye shi.




Kuskure ne bayan an yaye yaro andauki yaro akai shi gidan kakanni sabida, kawai dan ya manta da nono, bayan kin yaye yaro har yanzu Yana da bukatar kulawar ki.




Yaro ya saba da ke idan ya daina ganin ki zai shiga stress , kullum kuka yanaso yaga mamarsa , ba cin abinci sai aga yaro yana ramewa sosai , bayan kwana kadan yaro ba lafiya , babu abinci immunity duk sunyi weak , ana zuwa asibity sai ace Malnutrition.


0/Post a Comment/Comments

Previous Post Next Post

header

Sponsor