Farashin shinkafa zai fadi warwas a Nijeriya






Farashin shinkafar zai iya faduwa warwas a Nijeriya kungiyar manoma shinkafa

(RIFAN).




Ƙungiyar Manoman Shinkafa ta Ƙasa (RIFAN), tace bayan shugaba Buhari ya ƙaddamar Dalar Samfarerar Shinkafa a Abuja, ranar Talata.




Shugaban Kwamitin Tara Tulin Dalar Shinkafa na RIFAN ya shaida wa Kamfanin Dillacin Labarai na Ƙasa (NAN) cewa tara wanann irin Dalar Shinkafa mai yawa haka ya nuna cewa Najeriya za ta iya ciyar da kan ta.




A jiya Talata ne dai Shuagaba Buhari ya Æ™addamar da Dalar Shinkafa, a taron da manyan jami’an gwamnati su ka halarta, har da Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele.




An tara tulin dalar shinkafa Samfarera mai tarin yawa a daidai Shoprite na Lugbe da ke kan hanyar zuwa Babban Filin Jirgin Sama na Abuja.




Buhunan Samfarerar dai ba a cashe su ba, kuma an tara har buhu miliyan É—aya cur, waÉ—anda aka É—auko daga jihohi da daban-daban na Æ™asar nan, a Æ™arÆ™ashin shirin ‘Anchor Borrowers’ na CBN.




Mu’azu ya ce za zaran an kammala Æ™addamar da Dalar Shinkafa É—in, za a raba ta ga masu sarrafa shinkafa daban-daban a Æ™arÆ™ashin RIFAN.




“RIFAN ce tare da haÉ—in guiwar Ƙungiyar Masu Sarrafa Shinkafa ta Najeriya, za su cashe shinkafar sannan su sayar da ita a farashi mai sauÆ™i ga jama’a.” Inji shi.




“Za mu shiga gaba domin mu ga mun tabbatar da farashin shinkafar da ake nomawa a gida ya faÉ—i Æ™asa warwas, da zaran an fara tunkuÉ—a wannan shinkafar a cikin kasuwanni.




“Dama kuma yarjejeniyar da muka yi da Ƙungiyar Masu Cashe Shinkafa cewa za su sayar da ita a farashi mai rahusa ga ‘yan Najeriya.




“Duk da dai ba za mu iya magana a kan farashin da za a yanke ba, duk dai da cewa a yanzu farashin kayan abinci ya cilla sama sosai.




“Amma dai ina tabbatar maku cewa shinkafa za ta fi kowane irin abinci arha a Æ™asar nan, sakamakon wannan gagarimin shiri.” Inji shi.




Ya ce “shirin ‘Anchor Borrowers’ shaida ce cewa Gwamnatin Tarayya ta magance matsalar kayan abinci.” Domin idan zamu iya noma abinda zamu ci har mu sayar ba tare da mun shigo da shinkafa ba hakan na nufin nan gaba Nijeriya zata iya rike kasashen Afirka.




Yanzu duniya ta canza dole sai mun karfafi kamfanonin mu cikin gida kuma mun samar ma kan mu abin sayar wa mun dai na dogara da kasashen ketare kafin muyi maganin matsalolin mu da kan mu

0/Post a Comment/Comments

Previous Post Next Post

header

Sponsor