Hukumar NDLEA Ta Kama Tramadol Milyan Daya Da Rabi A Kan Hanyarsu Ta Zuwa Kano

Hukumar NDLEA Ta Kama Tramadol Milyan ÆŠaya Da Rabi A Kan Hanyarsu Ta Zuwa Kano Da Kebbi


...Hukumar ta kama bindigogi, harsashi, kuɗi da ƙwayoyi da dama a jihohi bakwai


A ƙalla kwayoyi miliyan ɗaya da dubu ɗari biyar na Tramadol, Exol-5 da kuma Diazepam wadanda aka yi lodin su daga Onacha a jihar Anambra zuwa Yauri, jihar Kebbi sun shiga hannun hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi, NDLEA, a ranar jumma'a 14 ga watan Janairu. Kazalika an samu nasarar kama kwayoyin Diazepam guda 425,000 a Segemu, jihar Kano.


An kuma kama wani É—an bindiga dadi kuma mai safarar kwayoyi a jihar Filato da kuÉ—aÉ—e wanda yawan su ya kai Naira 1,413,344 tare da makamai da harsashi.


A ranar Jumma'a, 22 ga watan Janairu, Jami'an hukumar ta hanyan bayanan sirri suka chafke wata tirela da ta taso daga Onacha zuwa Yauri na jihar Kebbi. Biyo bayan binciken motar da jami'ai suka yi, an samu Æ™wayoyi daban daban da aka boye su a cikin kayan kasuwa. Kwayoyin sun hada da kafso 394,480  da kwayoyi 3,000 na Tramadol wadanda nauyin su ya kai 83.707kg; kwayoyin Exol-5 guda 647,500 masu nauyin 203.315kg; Diazepam  guda 12,500 wanda nauyin su ya kai 2.05kg; Æ™wayoyin Bromazepam guda 1,500 da nauyin 0.45kg; kwalaben Codeine guda 999 masu nauyin 134.865kg, allurar pentazocine guda 4,000 masu nauyin 16.64kg. Kazalika an kama mutane uku: direbar motan mai suna Bashir Lawali mai shekaru 30, Abubakar Sani mai shekaru 30 da Ali Abubakar mai shekaru 19, yayinda su kuma na kano aka same su a wurin wani Sa'idu Yahya.


Hukumar ta kuma daÆ™ile yunÆ™urin  fitar da ganyen wiwi (34.05kg) wadanda aka boye su a cikin ma'ajiyi zuwa Æ™asar Ingila ta hanyar kamfanin NAHCO a filin jirgi na Murtala Mohammed dake birnin Ikko a Legas, a ranar 8 ga watan Janairu. A É—aya bangaren kuma, Hukumar ta NDLEA ta dakile ganyen wiwi wadda aka yi yunÆ™urin turawa Æ™asar Amurka a filin jirgin na Lagos. Yanzu haka mutane uku ne suke hannu akan waÉ—annan laifuka. 


A wani yunÆ™uri mai kama da wannan, hukumar ta daÆ™ile yunÆ™urin masu safarar miyagun Æ™wayoyi na shigo da Æ™unshin wiwi guda 94 wanda nauyin su ya kai 43.4kg zuwa Nijeriya ta tashar jirgin ruwa dake Tincan a Lagos. Haka kuma a wani yunÆ™uri mai kama da wannan, hukumar ta kama colorado guda wanda nauyin sa ya kai (17.3kg) a boye a cikin mota kirar Benz wacce aka shigo da ita daga Canada. 


A jihar Filato, an kama wani jami'in tsaro na bogi mai suna Babagana Maaji inda jami'ai suka bi sawun saƙon sa na wiwi har zuwa inda yake. Haka kuma a ranar talata 11 ga watan Janairu, jami'an hukumar ta jihar Filato sun kama wani da ake zargin ɗan bindiga ne mai suna Abdullahi Usman Ahmad a Hwolshe ɗauke da bindiga ƙirar Beretta Pistol, harsashi bakwai, gidan harsashi biyu, wiwi mai nauyin gram 12, ankwa guda daya da kudi Naira 1,136,344 wanda ake zargin kuɗin fansa ne da ya karba da kuma mota kirar Opel mai lamba ZAE35LQ.


Har yanzu dai a jihar ta Filato, jami'an hukumar NDLEA sun kama wani Æ™asurgumin mai fataucin hodar iblis mai suna Chibueze Okoro John dan shekaru 42, dauke da hodar iblis, Tramadol da mota Æ™irar Sienna Bus (BWR 584 AL) da kudi Naira 277,000 wanda ya bawa jami'an hukumar a matsayin cin hanci. 

KARANTA:

A jihar Delta dake Kudancin Nijeriya, an daÆ™ile yunÆ™urin Ejike Obiora na shigar da hodar iblis da heroin zuwa gidan gyara hali na Ogwashi-Uku, a  Æ™aramar hukumar Aniocha ta kudu a ranar 8 ga watan Janairu. Mutumin yayi yunÆ™urin shigar da Æ™wayoyin ne a cikin abinci da zai kaiwa wanda ke cikin gidan yarin. 


A jihar Ondo kuma, Jami'an hukumar sun kama wiwi wanda yawan sa ya kai 598kg a wani sumame da suka kai a garin Owo inda aka kama mutane biyu: Arataye Raimi dan shekaru 41 da Tope Osinnuwa mai shekaru 36. 


Wani mai suna Abdullahi Mohammed a Potiskum na jihar Yobe ya shiga hannu shi ma, inda aka kama shi da Æ™ulli-Æ™ulli na wiwi guda 48.5 yayin da shi kuma Dike Davison da aka kama shi a Aliade na jihar Benue É—auke da gram 50 na wiwi, da harsashi guda  29. 


A birnin tarayya Abuja, hukumar ta NDLEA ta kama wani mai suna Habib Yusif mai shekaru 41, É—auke da wiwi wanda yawan sa ya kai 28.2kg. A jihar Osun kuma, hukumar ta kama Samuel Joseph, Francis Ujor da Sola Johnson a Æ™auyen Onikoko dake Ile-Ife dauke da buhunan 100 na wiwi wanda yawan su ya kai 1,530  a ranar 13 ga watan Janairu.


Shugaban hukumar NDLEA Burgediya Janar Mohamed Buba Marwa mai ritaya ya jinjinawa jami'an inda yace hazaÆ™a da suka nuna ba zai tafi ba tare da jinjinawa na musamman ba. 


Mahmud Isa Yola

Hedikwatar NDLEA, Abuja

16 Janairu, 2022





 

0/Post a Comment/Comments

Previous Post Next Post

header

Sponsor