GWAJE-GWAJEN LAFIYA DA YA KAMATA MASOYA SUYI KAFIN AURE


NAU’O’IN GWAJE-GWAJEN LAFIYA DA YA KAMATA MASOYA SUYI KAFIN AURE


Masana sun bayyana cewa ana yin gwaje-gwajen lafiya ne kafin aure a kan nau’o’in cututtuka guda biyar:

1. Gwaji don tabbatar da ku6uta daga cututtukan da ke qetare mai shi zuwa waninsa a dalilin mu’amala ta jima’i (Sexually Transmittable Diseases – STDs), kamar:

HIV,

Hepatitis B,

Hepatitis C,

Gonorrhoea,

Syphilis.


2. Gwaji game da rukunin kwayoyin halitta (genes) don sanin Genotype din masu niyyar yin aure a matsayin “AA”, “AS”, ko “SS” don tabbatar da ku6uta daga cututtukan da ke bin hanyoyin jini wajen yin naso da shafar abokin zama ko ‘ya‘yan da za a haifa kamar cutar Anaemia (sickle cell disease).


3. Gwaji don gane rukunin jini: ‘A’, ‘B’, ‘0’ ko ‘AB’, da danginsa na Rhesus factor (positive, ‘+’ ko negative, ‘-‘). Kasancewar bincike ya nuna cewa macen da ke qarqashin dangin jini na Negative idan ta aure wanda ke qarqashin Positive, tana iya fuskantar hatsarin yawan zubewar ciki ko mutuwar dan da ke cikin mahaifa (intrauterine death). Gudanar da irin wannan gwajin na da muhimmanci.

KARANTA:

4. Gwaji don tabbatar da rashin aibobin da ke sa a kai ga raba aure a tsakanin miji da mata, kamar cututtukan da ke iya jawo rashin haihuwa, da kuturta, da wasu nau’o’in cutar daji (cancer) masu hatsari, da cutar qoda.


5. Gwaji game da cututtukan da a ke gado, wadanda aka ce a yanzu adadinsu ya kai 8000. Irin wadannan cututtuka sun hada da ciwon hauka, da ciwon ido da ‘ya‘ya ke iya gado daga iyaye kamar glaucoma.

Daga Aliyu Samba 

0/Post a Comment/Comments

Previous Post Next Post

header

Sponsor