MAGANIN KARFIN MAZA

 

ZAUREN FIQHU


MAGANIN KARFIN MAZA

TAMBAYA TA 2017


********************

Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu da fatan Malam ka tashi lafiya, Allah ya kara hakuri da imaani.


Allah gafarta Mallam. Ina neman maganin karfin maza wanda bazai kawo side effect ba da yadda zai sa abun Namiji ya kara girma. Nagode

AMSA

*******

Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.


Shi maganin Qarin kuzarin Namiji, ya bambanta ne daga wani mutumin zuwa wani. Misali maganin da wani yasha yaji dadinsa, ba lallai ne kai idan kasha yayi maka aiki ba. Amma dai ga wasu abubuwan da mun ta'ba yin bayaninsu anan Zauren Fiqhu kuma mutane da dama sunce sunyi amfani dasu kuma sunji dadi :

KARANTA:

1. MAN HABBATUS SAUDA : Ka samu shayin Na'a-Na'a wanda aka sanya Na'a-Na'a din sosai. Ka zuba masa Man Habbatus Sauda cokali 1, sannan kasha. Safe da dare kafin kwanciya.


Ko kuma ka samu Qwan Tattabara ko Qwan Kazar gida guda biyu ko uku, Ka zuba garin habbatus Sauda cokali guda aciki. Agauraya a soyashi da Man Habbatus Sauda ko Zaitun, sannan kaci.


2. SAIWAR GINSENG : Wani itace ne ingantacce wanda ake kawoshi daga Qasar China. Idan Namiji ya yawaita amfani dashi zai samu Qarin Kuzari da girma.


3. KANKANA : Kankana tana kunshe da irin sinadarin dake cikin Kwayoyin Viagra. Don haka tana Qara Qarfin Namiji sosai, kuma 'Ya'yanta suna Qara ma Namiji girma ba tare da wata illa ga jikinsa ba.


Ka samu Qatuwar Kankana ka yanka bayan Magriba ko Isha'i ka shanyeta gaba daya. Kuma ka rika taunewa kwallon. In sha Allahu zaka ji bambanci mai yawa.


4. RUWAN CITTA : Ka samu Madarar Peak ko Luna, ka tsiyaya ruwan chitta ko kuma garinta daidai misali. Sannan ka samu garin Kustul Hindi cokali guda ka zuba aciki, sannan ka sanya zuma daidai Misali sannan ka shanye, Minti 30 kafin kwanciya.


5. MAN JIRJEER : Yawancin Maza masu fama da raunin Mazakuta, Basur ne ke damunsu ko kuma Majinar Kwankwaso (Waist).


Shi Man Jirjeer yana Qone irin wannan Majinar ne, har majinar Qirji. Don haka yana Qara ma Namiji Qarfi.


Wadanda suke zaune a Qasashen Larabawa kamar Saudia ko Misra zasu iya samun ganyensa cikin sauki. Domin shi suke sanyawa a saman abincinsu kamar yadda muke amfani da Lettuce anan.


6. ZOGALE : Bawon jikin itacen Zogale idan aka shanyashi aka dakashi, ana hadawa da Madara ko Zuma ana sha. Shima yana Qara kuzarin Namiji sosai.


ABIN LURA

************

Yawancin wadannan Magungunan ba wai daga yin amfani dasu sau daya ko sau biyu zaka ga chanji gaba daya ba. Dole sai ka juri amfani dasu yau da kullum kana hadawa da Motsa jiki, kuma ka rage amfani da abincin zamani wadanda suke kunshe da sinadarai masu Qarfi. Irin su Lemon kwalba, Biscuits, Chocolate, Alawa, Succarine, Farin Magi, etc.


Ka koma amfani da kayan sha irin na gargajiya kamar irin su Kunun aya, Mazarkwaila, 'Ya'yan itace irin su gwanda, ayaba, Lemo, Karas, etc.

Allah yasa mu dace.

WALLAHU A'ALAM.


DAGA ZAUREN FIQHU 31-10-2016 (29-01-1438)

DON GIRMAN ALLAH KAR WANI YA CHANZA MANA ABINDA MUKA RUBUTA ZUWA GA SON RANSA. ('Barayin Fasaha aji tsoron Allah dai).

0/Post a Comment/Comments

Previous Post Next Post

header

Sponsor