Gwamnatin Jihar Zamfara ta ce an kama wasu jami'an tsaro bakwai a jihar bisa zarginsu da taimaka ayyukkan fashi da makami a sassa daban-daban na jihar. Gwamnatin ta sanarda haka ne a yayin wani taron manema labarai da ma'aikatun watsa labarai da harkokin tsaron na jihar suka gudanar a yau.
A sanarwar da gwamnatin ta raba wa manema labarai ta ce jami'an tsaron bakwai sun fuskanci tambayoyi kuma sun amsa laifukkansu da suka hada kyankyasawa 'yan ta'adda bayanan sirri na soji da samar musu makamai da kakin soji da sauran abubuwan da suke bukata.
Ta ce tuni aka mika wadannan jami'an tsaron bakwai ga hukumomin da abin ya shafa domin daukar mataki a kansu.
In ji sanarwar,daga cikinsu wanda aka kama yana kokarin mikawa wani rikkaken dan fashi mai suna Kabiru Bashiru albarusai 20 da ya saida masa bayan ya biya shi kudi Naira dubu 100.
Ta ce na biyu kuwa wanda ya fito daga jihar Sakkwato, an kama shi yana kai wa 'yan fashin da uniform da sauran wasu abubuwan da sojoji ke amfani da su.
Yayin da aka kama shin, an samu da rigunan da harsashe bai ratsawa guda tara da kakin soja guda hudu da katin shaidar zama sojan Najeriya da sauransu.
Daga cikin wadanda aka kaman kuma har wayau akwai wani likita da aka samu da takalamin soja taki 10 da garkuwar kwabri da kuma safar hannu seti biyar.
Sanarwar ta ce wannan kamen ya tabbatar da maganar da gwamnan jihar ya taba yi a baya cewa jama'a za su sha mamaki idan suka ji wadanda ke daurewa ta'addacin gindi a jihar da ma makwabtanta.
Daga karshe sanarwar ta ce gwamnatin jihar ta Zamfara na rokon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ya cika alkawalin da ya yi na tura bataliya shidda ta sojoji zuwa jihar domin kawar da 'yan fashin da suka ki yarda da sulhu wadanda ke ci gaba da addabar al'umomin yankunan karkara a jihar.
Source: BBC Hausa
DAGA Net Age Blog
https://chat.whatsapp.com/HYg2KvNxf2kI2IuVfqh5RH
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
https://www.facebook.com/netage001/
Post a Comment