MAGANIN KAIKAYIN GABA



MAGANIN KAIKAYIN GABA DA MATSEMATSI



Matsalar kaikayin MATSE- MATSI, abu ne wanda yake damun mutane da yawa Maza da mata. Insha Allah zamuyi bayanin yadda matsalar take, da kuma yadda za'a magance ta. 

Matsalar kaikayin gaba da kaikayin matse-matskamafata ruwa bisa dalilai kamar haka: 

1. Akwai wasu irin Kwayoyin halittu na bacteria wadanda suke rayuwa ajikin 'Dan Adam.

Karanta:

wasu daga cikin jikinsa, wasu kuma daga waje akan fatarsa. Mafiya yawa daga cikin wadannan Kwayoyin Bacteria din bassu cutarwa. amma akwai 'Yan Qalilan masu cutarwa. To su dai bacteria sun fi son zama ne awajen da yaje da damshi-damshi. Kamar cikin dubura, ko al'aurar mace, ko kuma acikin matse-matsi. Taruwarsu acikin matse matsin mutum shi ke kawo masa kaikayi awajen. kuma da zarar mutum ya sosa, sai fatar wajen ta Qara yin kauri. sai kuma kaikayin ya Qaru. Da haka da haka duk lokacin da kayi susa sai fatar wajen ya Qara kauri da damshi-damshi. Sai su kuma bacteria din su ci gaba da haihuwa awajen. 

2. KYASBI (ECZEMA) Shi ma idan ya kamafatar MATSE MATSI akan samu wannan kaikayin. 

3. KAURIN JIKI: Wato Qiba.

idan mutum yana da Qiba, to dole zai rika yawan yin gumi (zufa) kuma matse matsinsa zai rika tara damshi. don haka bacteria ta samu wajen zama kenan. sai ya haifar masa da kaikayin matse-matsi da kaikayin gaba. 


MAGANI :

hanyoyin magance

matsalar sun hada da: 

1. Yin Wanka akan lokaci.

2. Tabbatar da cewa matse-matsinka ya bushe kafin ka sanya suturarka.

3. Ka dena sanya Underwear ko wanduna matsattsu.

4. Ka nemi Anti Fungal Creams ko Powder sun nan a chemists ana satakea.

5. Ka guji yin wanka da garin sabulu (detergents) irin su Omo sauransu. anyi su ne domin wanki ba wai wanka ba. Kuma amfani dasu zai rage ma fatar jikinka Quality. 

6. Ka samu ruwan danyen zogale ka rika gogawa awajen. shima zai yi maka maganu sosai.

7. Man Habbah, Man Zaitun, idan aka sanyasu akan fatsr wajen za'a samu.
sauki sosai. Allah ya sawwake.


Source: Yan Mayan zamani

0/Post a Comment/Comments

Previous Post Next Post

header

Sponsor