Boko haram: Sojoji sunyi nasaran kashe Abu Aisha da wasu manyan kwamandojin ISWAP 17 a Garin Damasak




Boko haram: Dakarun Sojojin Nigeria sun kashe babban kwamandan kungiyan ISWAP, Bukar Gana Fitchmeram Wanda akafi sani da (Abu A'isha) da wasu mayakansa da suka zo ramuwar gayya a Damasak amma suka haÉ—u da ajalinsu hannun sojoji a ranar Alhamis.



Rundunar Sojin ta ce ƴan ta'addan sun gamu da karshen su a yayin da suka kai hari bayan kashe manyan kwamandojin ISWAP 12 a ƙaramar hukumar Mobbar sakamakon hare-haren ƙasa da sama da sojojin suka shafe yi na kwanaki 7.

Kakakin soji, Birgediya Janar Mohammed Yerima, ne sanar da hakan ta shafin Twitter na rundunar a ranar Juma'a.

Karanta:
A baya an ruwaito cewa Æ´an ta'addan sun kashe wasu sojoji sun kuma lalata ginin Majalisar Dinkin Duniya yayin harin da suka kai Damasak amma Yerima, a ranar Juma'a ya ce an kashe manyan kwamandojin ISWAP da jiragen yaki yayin harin.

Ya yi wa sanarwar laƙabin 'Yadda manyan kwamandojin ISWAP suka gamu da ƙarshen su yayin da suka dawo ɗaukan fansa a Damasak.'

Sanarwar ta ce, "Hare-haren sama da aka kai a Tudun Wulgo, Zafi, da Tumbun Alhaji, Kusuma, Sigar a Ngala da Arijallamari a Abadam, Marte a ƙaramar hukumar Ngala ya yi sanadin kashe manyan kwamandojin ISWAP.

"Kwamandojin da aka kashe yayin harin saman sun hada da Mohammad Fulloja, Ameer Mallam Bello, Ba'a kaka Tunkushe , Abu Muktar Al-Ansari, Ameer Abba Kaka, Abu Huzaifa, Ameer Modu Kwayem, yayin da Goni Mustapha wanda shine babban limamin ISWAP ya tsira da raunin harsashi."

Rundunar sojojin ta kara da cewa hare-haren sama da ƙasa da aka kai a ranar 6 ga watan Afrilu ya yi sanadin mutuwar manyan kwamandojin ISWAP biyu ciki har da Abu-Rabi da Muhammed Likita da masu tsaronsu a kusa da Kusuma, Sigir a ƙananan hukumomin Ngala da Arijallamari, Abadam.

An kuma lalata wuraren da Æ´an ta'addan ke ajiye makamansu yayin samamen da dakarun Operation Lafiya Dole suka kai.

A daren ranar 10 ga watan Afrilu, Yerima ya yi bayanin cewa dakarun Sojojin sun ritsa wasu kwamandojin yan ta'addan uku a kusa da Wulgo/Logomani kusa da iyakar Kamaru yayin da suke kokarin satar shanun mutanen yakin, wadanda aka kashe sune Ameer Umar, Abu Ubaida da Abu Salim.

A cewarsa, wannan illar da aka yi wa Æ´an ta'addan ya saka sun fara kai hare-hare suna satar abinci da magunguna don kulawa da yan uwansu da suka jikkata.

Har wa yau, rundunar sojin ta ce a ranar 11 ga watan Afrilu, sojojin sun halaka wasu Æ´an ta'addan a cikin motocci masu bindiga 5 a Damasak.

Ya ce an wasu daga cikin Æ´an ta'ddan sun samu shiga garin na Damasak inda suka kone gine-gine suka sace kaya kafin suka tsere.

Wannan ba shine karo na farko da aka kai hari Damasak ba amma duk da hakan sojojin na cike da izza a yakin da suke yi da Æ´an ta'addan duk da akwai Æ´an leken asiri da ke sanar da Æ´an ta'addan inda sojojin suke.

Source: Legit Newspapers

0/Post a Comment/Comments

Previous Post Next Post

header

Sponsor