Pantami ya cire takunkumin rijistan layin waya, yace a cigaba da gashi




Gwamnatin tarayya ta bada izinin cigaba da rijistan sabbin layukan waya bayan wata da watanni da sanya takunkunmin yin haka.


Ministan Sadarwa, Dakta Isa Ibrahim Ali Pantami, ya bayyana hakan ne ta bakin hadiminsa, Dr Femi Adeluyi, ranar Alhamis a shafin twitter.

Ministan ya ce za'a cigaba da rijistan amma da sharadin sai mutum na da lamban katin zama dan kasa, NIN.

Pantami ya ce an yanke shawaran cigaba da rijistan sabbin layuka ne bayan amincewar shugaba Buhari da sabon tsarin rijistan layuka da ma'aikatarsa ta samar.

"An kammala gyara-gyare kan tsarin bisa ga umurnin shugaban kasa inda aka wajabta amfanin da lambar NIN don rijisttan sabon layi a jiya, 14 ga Afrilu, 2021," jawabin yace.

"Dr Pantami ya gabatar da tsarin ga shugaba Muhammadu Buhari...kuma (Buhari) ya jinjinawa ministan bisa kokarinsa wajen kawo cigaba sashen tattalin arzikin zamani da kuma atisayen hada layukan waya da NIN."

"Za'a fara aiwatar da sabon tsarin ranar Litnin, 19 ga Afrilu 2021. Hakazalika za'a cigaba da bada sabbin layuka da kuma sauran abubuwan da aka dakatar a ranar.

"Bugu da kari, Ministan ya umurci NCC da NIMC su tabbatar da cewa maus rijistan layukan da jama'a sun bi tsarin sau da kafa."

Source: legit.ng

DAGA Net Age Blog


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/HYg2KvNxf2kI2IuVfqh5RH

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

https://www.facebook.com/netage001/ 


0/Post a Comment/Comments

Previous Post Next Post

header

Sponsor